Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.“Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? SelaKu tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.“Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya.“Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ne.Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.”Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne.