Zabura 43

Ka nuna ni marar laifi ne, ya Allah, ka kuma nemi hakkina a kan al’ummai marasa sanin Allah. Ka kuɓutar da ni daga masu ruɗu da mugayen mutane. Kai ne Allah mafakata. Me ya sa ka ƙi ni? Me zai sa in yi ta yawo ina makoki, a danne a hannun abokin gāba? Ka aiko da haskenka da gaskiyarka, bari su bishe ni bari su kawo ni ga dutsenka mai tsarki, zuwa wurin da kake zama. Sa’an nan zan tafi bagaden Allah, ga Allah, farin cikina da murnata. Zan yabe ka da garaya, Ya Allah, Allahna. Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da Allahna.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

订阅我们的新闻通讯

及时了解新的资料页、活动与平台更新。