Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; bari kukata ta neman taimako ta zo gare ka.Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni sa’ad da nake cikin damuwa. Ka juye kunnenka gare ni; sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri.Gama kwanakina sun ɓace kamar hayaƙi; ƙasusuwana suna ƙuna kamar jan wuta.Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa; na manta in ci abinci.Saboda nishina mai ƙarfi na rame na bar ƙasusuwa kawai.Ni kamar mujiyar jeji ne, kamar mujiya a kufai.Na kwanta a faɗake; na zama kamar tsuntsun da yake shi kaɗai a kan rufin ɗaki.Dukan yini abokan gābana suna tsokanata; waɗanda suke mini ba’a suna amfani da sunana yă zama abin la’ana.Gama ina cin toka a matsayin abincina ina kuma gauraye abin sha nawa da hawayesaboda fushinka mai girma, gama ka ɗaga ni sama ka yar a gefe.Kwanakina suna kamar inuwar yamma; na bushe kamar ciyawa.Amma kai, ya Ubangiji, kana zaune a kursiyinka har abada; sunan da ka yi zai dawwama a dukan zamanai.Za ka tashi ka kuma ji tausayin Sihiyona, gama lokaci ne na nuna alheri gare ta; ƙayyadadden lokacin ya zo.Gama duwatsunta suna da daraja ga bayinka; ƙurarta kawai kan sa su ji tausayi.Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji, dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka.Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyona ya kuma bayyana a ɗaukakarsa.Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi; ba zai ƙyale roƙonsu ba.Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa, cewa mutanen da ba a riga an halitta ba za su yabi Ubangiji,“ Ubangiji ya duba ƙasa daga wurinsa mai tsarki a bisa, daga sama ya hangi duniya,don yă ji nishe-nishen’yan kurkuku yă kuma saki waɗanda aka yanke musu hukuncin mutuwa.”Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyona yabonsa kuma a Urushalimasa’ad da mutane da mulkoki suka tattaru don su yi wa Ubangiji sujada.Cikin rayuwata, ya karye ƙarfina; ya gajartar da kwanakina.Sai na ce, “Kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina, ya Allah; shekarunka suna bi cikin dukan zamanai.A farkon fari ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne.Za su hallaka, amma za ka ci gaba; duk za su tsufe kamar riga. Kamar riga za ka canja su za a kuwa zubar da su.Amma kana nan yadda kake, kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba.’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka; zuriyarsu za su kahu a gabanka.”