1Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji. 2Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki ku kuma yabi Ubangiji. 3Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa, ya albarkace ku daga Sihiyona.