Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki.Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub.Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke Ya birnin Allah, Sela“Zan lissafta Rahab a cikin waɗanda suka san ni, Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush, zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ”Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce, “Wannan da wancan an haifa a cikinta, Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.”Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa, “An haifi wannan a Sihiyona.” SelaYayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera, “Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.”