Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni, dare da rana ina kuka a gabanka.Bari addu’ata ta zo a gabanka; ka kasa kunne ga kukata.Gama raina yana cike da wahala rayuwata tana gab da kabari.An lissafta ni cikin waɗanda suka gangara zuwa cikin rami; ni kamar mutumin da ba shi da ƙarfi ne.An ware ni tare da matattu, kamar waɗanda aka kashe da suke kwance a kabari, waɗanda ba ka ƙara tunawa, waɗanda aka yanke daga taimakonka.Ka sa ni a ramin da yake can ƙasa cikin zurfafa mafi duhu.Hasalarka tana da nauyi a kaina; ka turmushe ni da dukan raƙumanka. SelaKa ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni ka sa na zama abin ƙyama a gare su. An kange ni, ba yadda zan kuɓutaidanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki. Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana; na tā da hannuwana zuwa gare ka.Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne? Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne? SelaAna furta ƙaunar a cikin kabari ne, ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne?An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne, ko ayyukan adalcinka a lahira?Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji; da safe addu’ata kan zo gabanka.Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni?Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu; na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya.Hasalarka ta sha kaina; razanarka ta hallaka ni.Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa; sun mamaye ni ɗungum.Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni; duhu ne abokina na kurkusa.