Zabura 130

Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji; Ya Ubangiji, ka ji muryata. Bari kunnuwanka su saurara ga kukata ta neman jinƙai. In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai, Ya Ubangiji, wa zai tsaya? Amma tare da kai akwai gafartawa, saboda haka ake tsoronka. Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata. Raina na jiran Ubangiji fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya, fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya. Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji, gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa. Shi kansa zai fanshi Isra’ila daga dukan zunubansu.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

订阅我们的新闻通讯

及时了解新的资料页、活动与平台更新。