Zabura 82

Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”. “Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? Sela Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya. Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye. “Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya. “Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ne. Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.” Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

Prenumerera på vårt nyhetsbrev

Håll dig uppdaterad om nya profiler, evenemang och plattformsnyheter.