Yabi Ubangiji. Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro.Ayyukan Ubangiji da girma suke; dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu.Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne, adalcinsa kuma zai dawwama har abada.Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa; Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma.Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa; yakan tuna da alkawarinsa har abada.Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa, yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai.Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya; dukan farillansa abin dogara ne.Tsayayyu ne har abada abadin, ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya.Yana ba da ceto ga mutanensa; ya kafa alkawarinsa har abada, tsarki da banrazana ne sunansa.Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima; dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau. Gare shi ne madawwamin yabo.