Zabura 134

Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji. Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki ku kuma yabi Ubangiji. Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa, ya albarkace ku daga Sihiyona.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

S'abonner à notre newsletter

Restez informé des nouveaux profils, événements et mises à jour de la plateforme.