Zabura 67

Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Sela don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai. Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka. Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. Sela Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe. Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu. Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

뉴스레터 구독

새로운 프로필과 행사, 플랫폼 소식을 받아 보세요.