Zabura 126

Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona, mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki. Bakunanmu sun cika da dariya, harsunanmu da waƙoƙin farin ciki. Sai ana faɗi a cikin al’ummai, “ Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.” Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu, mun kuwa cika da farin ciki. Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji kamar rafuffuka a Negeb. Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki. Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

뉴스레터 구독

새로운 프로필과 행사, 플랫폼 소식을 받아 보세요.