Zabura 120

Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata, ya kuwa amsa mini. Ka cece ni, ya Ubangiji, daga leɓuna masu ƙarya da kuma daga harsuna masu yaudara. Me zai yi maka, me kuma ya fi, ya kai harshe mai yaudara? Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi, tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya. Kaitona da nake zama a Meshek, da nake zama a ciki tentunan Kedar! Da daɗewa na zauna a cikin waɗanda suke ƙin salama. Ni mutum ne mai salama; amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

뉴스레터 구독

새로운 프로필과 행사, 플랫폼 소식을 받아 보세요.