Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce,sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba.Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi.Amma Ubangiji mai adalci ne; ya’yantar da ni daga igiyoyin mugaye.Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya.Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma;da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”