Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Seladon a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka.Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. SelaBari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe.Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.