Yabi Ubangiji. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji.Bari a yabi sunan Ubangiji, yanzu da har abada kuma.Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa, a yabi sunan Ubangiji.Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai, ɗaukakarsa a bisa sammaiWane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu, Wannan mai zama a kursiyi can bisa,wanda yake sunkuya yă dubi sammai da duniya?Yakan tā da matalauta daga ƙura yakan ɗaga mabukata daga tarin toka;ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu.Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta ta zama kamar mahaifiyar’ya’ya mai farin ciki. Yabi Ubangiji.