Zabura 129

Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce, sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba. Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi. Amma Ubangiji mai adalci ne; ya’yantar da ni daga igiyoyin mugaye. Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya. Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma; da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa. Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

الاشتراك في نشرتنا الإخبارية

ابقَ على اطلاع بالملفات الجديدة والفعاليات وتحديثات المنصة.