Zabura 113

Yabi Ubangiji. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji. Bari a yabi sunan Ubangiji, yanzu da har abada kuma. Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa, a yabi sunan Ubangiji. Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai, ɗaukakarsa a bisa sammai Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu, Wannan mai zama a kursiyi can bisa, wanda yake sunkuya yă dubi sammai da duniya? Yakan tā da matalauta daga ƙura yakan ɗaga mabukata daga tarin toka; ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu. Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta ta zama kamar mahaifiyar’ya’ya mai farin ciki. Yabi Ubangiji.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

Subscribe to our newsletter

Stay updated with new profiles, events, and platform updates.