Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni!Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” SelaAmma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. SelaNa kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye.Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela