Zabura 121

Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai, ta ina ne taimakona zai zo? Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa. Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba; tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci. Ubangiji yana tsaronka, Ubangiji ne inuwa a hannun damanka; rana ba za tă buge ka cikin yini ba balle wata da dare. Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa, zai tsare ranka; Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

ニュースレターを購読する

新しいプロフィール、催し、プラットフォームの更新情報をお届けします。