Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata.Daga iyakar duniya na yi kira gare ka, na yi kira yayinda zuciyata ta karai; ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.Ina marmari in zauna a tentinka har abada in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. SelaGama ka ji alkawarina, ya Allah; ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka.Ka ƙara kwanakin ran sarki, shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa.Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada; ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi.Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka in kuma cika alkawarina kowace rana.