Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka.Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka.Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji.Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima,bari kuma ka rayu ka ga’ya’ya’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.