Zabura 3

Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni! Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” Sela Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina. Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni. Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba. Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye. Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

S'abonner à notre newsletter

Restez informé des nouveaux profils, événements et mises à jour de la plateforme.