Zabura 128

Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa. Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka. Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka. Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji. Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima, bari kuma ka rayu ka ga’ya’ya’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

Подписаться на нашу рассылку

Следите за новыми профилями, мероприятиями и обновлениями платформы.