Zabura 122

Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni, “Bari mu tafi gidan Ubangiji.” Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima. An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda. A can ne kabilu suke haurawa, kabilan Ubangiji, don su yabi sunan Ubangiji bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila. A can kursiyoyin shari’a yake tsaye, kursiyoyin gidan Dawuda. Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya. Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.” Saboda’yan’uwana da kuma abokaina, zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.” Saboda gidan Ubangiji Allahnmu, zan nemi wadatarki.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

Prenumerera på vårt nyhetsbrev

Håll dig uppdaterad om nya profiler, evenemang och plattformsnyheter.