Zabura 54

Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka; ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka. Ka ji addu’ata, ya Allah; ka saurari maganar bakina. Baƙi suna kawo mini hari; mutane marasa imani suna neman raina, mutanen da ba sa tsoron Allah. Sela Tabbatacce Allah ne mai taimakona, Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni. Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina; cikin amincinka ka hallaka su. Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka; zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau. Gama ya cece ni daga dukan wahalolina, idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

Unseren Newsletter abonnieren

Bleiben Sie über neue Profile, Veranstaltungen und Plattform-Updates informiert.