Zabura 23

Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba, Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa, yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya, yakan maido da raina. Yakan bi da ni a hanyoyin adalci saboda sunansa. Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya. Ka shirya mini tebur a gaban abokan gābana. Ka shafe kaina da mai; kwaf nawa ya cika har yana zuba. Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi dukan kwanakin raina, zan kuwa zauna a gidan Ubangiji har abada.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

Unseren Newsletter abonnieren

Bleiben Sie über neue Profile, Veranstaltungen und Plattform-Updates informiert.