Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,“Yaushe za ka gama maganganun nan? Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana.Don me muke kamar shanu a wurinka, ka ɗauke mu mutanen wofi?Kai da ka yayyage kanka don haushi, za a yashe duniya saboda kai ne? Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu?“An kashe fitilar mugu; harshen wutarsa ya daina ci.Wutar cikin tentinsa ta zama duhu; fitilar da take kusa da shi ta mutu.Ƙarfin takawarsa ya ragu; dabararsa ta ja fāɗuwarsa.Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga, yana ta yawo a cikin ragar.Tarko ya kama ɗiɗɗigensa; tarko ya riƙe shi kam.An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa; an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefe yana bin shi duk inda ya je.Masifa tana jiransa; bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi.Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa; ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa.An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsa aka sa shi tsoro sosai.Wuta ta cinye tentinsa; farar wuta ta rufe wurin da yake zama.Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasa rassansa sun mutu a sama.An manta da shi a duniya; ba wanda yake ƙara tunawa da shi.An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu, an kore shi daga duniya.Ba shi da’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa, ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama.Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi; tsoro ya kama mutanen gabas.Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake, haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.”