Zabura 114

Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar, gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe, Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah, Isra’ila mallakarsa. Teku ya kalla ya kuma gudu, Urdun ya juye da baya; duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai kamar tumaki. Me ya sa, ya teku, kika gudu, Ya Urdun, ka juya baya, ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna, ku tuddai, kamar tumaki? Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji, a gaban Allah na Yaƙub, wanda ya juye dutse ya zama tafki, dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

Assinar nossa newsletter

Mantenha-se a par dos novos perfis, eventos e novidades da plataforma.