Zabura 127

In ba Ubangiji ne ya gina gida ba, masu gininta suna wahala a banza ne. In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba, masu tsaro suna yin tsaro a banza. Banza ne ka farka da wuri ka koma da latti, kana fama don abincin da za ka ci, gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna. ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji, yara lada ne daga gare shi. Kamar kibiyoyi a hannun jarumi haka’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya. Mai albarka ne mutumin da korinsa sun cika da su. Ba za a kunyata su ba sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

Abonner på nyhetsbrevet vårt

Hold deg oppdatert på nye profiler, arrangementer og plattformnyheter.