Zabura 100

Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya. Yi wa Ubangiji sujada da murna; ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki. Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah. Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne; mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa. Ku shiga ƙofofinsa da godiya filayen gidansa kuma da yabo; ku gode masa ku kuma yabi sunansa. Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada; amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

Abonneer op onze nieuwsbrief

Blijf op de hoogte van nieuwe profielen, evenementen en platformupdates.