Waɗannan su ne sarakunan ƙasashen da Isra’ilawa suka ci da yaƙi, suka kuma mallaki ƙasarsu a gabashin Urdun, daga kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon haɗe da dukan gefen gabas na Araba.Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Ya yi mulki daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa, Kogin Yabbok, wanda yake iyakar Ammonawa. Wannan ya haɗa da rabin Gileyad.Ya kuma yi mulki a kan gabashin Araba daga tekun Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri), zuwa Bet-Yeshimot da kuma kudu zuwa gangaren dutsen Fisga.Haka ma suka ci sashen Og sarkin Bashan, ɗaya daga cikin Refahiyawa na ƙarshe da ya yi mulki a Ashtarot da Edireyi.Mulkinsa ya taso daga Dutsen Hermon, da Saleka, da dukan Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa haɗe da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar Heshbon ta sarki Sihon.Sai Musa, bawan Ubangiji da Isra’ilawa suka ci Sihon da Og da yaƙi. Musa bawan Ubangiji kuwa ya ba da ƙasarsu ga mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.Waɗannan su ne sarakuna da kuma ƙasashen da Yoshuwa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi a yammancin Urdun, daga Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa Seyir. Yoshuwa ya raba ƙasarsu ta zama gādo ga Isra’ilawa bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila.Ƙasar ta haɗa da ƙasar kan tudu, filayen arewanci, Araba, gangaren Dutse, da jejin, da kuma Negeb, wato, ƙasashen Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa, da Yebusiyawa.Sarkin Yeriko, ɗaya sarkin Ai (kusa da Betel), ɗayasarkin Urushalima, ɗaya sarkin Hebron, ɗayasarkin Yarmut, ɗaya sarkin Lakish, ɗayasarkin Eglon, ɗaya sarkin Gezer, ɗayasarkin Debir, ɗaya sarkin Bet-Gader, ɗayasarkin Horma, ɗaya sarkin Arad, ɗayasarkin Libna, ɗaya sarkin Adullam, ɗayasarkin Makkeda, ɗaya sarkin Betel, ɗayasarkin Taffuwa, ɗaya sarkin Hefer, ɗayasarkin Afek, ɗaya sarkin Sharon, ɗayasarkin Madon, ɗaya sarkin Hazor, ɗayasarkin Shimron Meron, ɗaya sarkin Akshaf, ɗayasarkin Ta’anak, ɗaya sarkin Megiddo, ɗayasarkin Kedesh, ɗaya sarkin Yokneyam a Karmel, ɗayasarkin Dor (A Nafot Dor), ɗaya sarkin Goyim a Gilgal, ɗayasarki Tirza, ɗaya. Duka-duka dai sarakuna talatin da ɗaya ne.