Zabura 52

Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum? Me ya sa kake fariya dukan yini, kai da kake abin kunya a idanun Allah? Harshenka kan shirya hallaka; yana nan kamar reza mai ci, kana ta ruɗu. Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri, ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. Sela Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa, Ya kai harshe mai ruɗu! Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka. Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka; zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Sela Masu adalci za su ga su ji tsoro; za su yi masa dariya, suna cewa, “Yanzu, ga mutumin da bai mai da Allah mafakarsa ba amma ya dogara a yawan arzikinsa ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!” Amma ni kamar itace zaitun ne ina haɓaka a gidan Allah; na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah har abada abadin. Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi; a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau. Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

Suscribirse a nuestro boletín

Manténgase al día de los nuevos perfiles, eventos y novedades de la plataforma.