Zabura 47

Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki. Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya! Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu. Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Sela Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni. Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai. Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi. Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki. Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai.

Hausa Contemporary Bible

copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc — CC-BY-SA-4.0 — CC-BY-SA-4.0

Suscribirse a nuestro boletín

Manténgase al día de los nuevos perfiles, eventos y novedades de la plataforma.