Ga lissafin waɗanda suka dawo daga bauta a Babilon, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwasa zuwa bauta a ƙasar Babilon (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowa ya koma garinsu.Sun komo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Serahiya, da Re’elaya, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba’ana). Ga jerin mazan mutanen Isra’ila.Zuriyar Farosh mutum 2,172ta Shefatiya 372ta Ara 775ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,812ta Elam 1,254ta Zattu 945ta Zakkai 760ta Bani 642ta Bebai 623ta Azgad 1,222ta Adonikam 666ta Bigwai 2,056ta Adin 454ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98ta Bezai 323ta Yora 112ta Hashum 223ta Gibbar 95.Mutanen Betlehem 123na Netofa 56na Anatot 128na Azmawet 42na Kiriyat Yeyarim, da Kefira Beyerot 743na Rama da Geba 621na Mikmash 122na Betel da Ai 223na Nebo 52na Magbish 156na ɗayan Elam ɗin 1,254na Harim 320na Lod, da Hadid da Ono 725na Yeriko 345na Sena’a 3,630.Firistoci. Zuriyar Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 973ta Immer 1,052ta Fashhur 1,247ta Harim 1,017.Lawiyawa. Lawiyawa na zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodawiya) mutum 74.Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 128.Masu tsaron haikali. Zuriyar Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita, da Shobai mutum 139.Ma’aikatan haikali. Zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot,Keros, Siyaha, Fadon,Lebana, Hagaba, Akkub,Hagab, Shamlai, Hanan,Giddel, Gahar, Reyahiya,Rezin, Nekoda, Gazzam,Uzza, Faseya, Besai,Asna, Meyunawa, Nefussiyawa,Bakbuk, Hakufa, Harhur,Bazlut, Mehida, Harsha,Barkos, Sisera, Tema,Neziya da Hatifa.Zuriyar bayin Solomon. Zuriyar Sotai, Hassoferet, Feruda,Ya’ala, Darkon, Giddel,Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Ami.Dukan zuriyar ma’aikatan haikali, da kuma bayin Solomon 392.Waɗannan mutanen ne suka zo daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addan da Immer, amma ba su iya nuna ainihin tushensu daga Isra’ila ba.’Yan zuriyar Delahiya, Tobiya, da Nekoda 652.Daga cikin firistoci kuma, zuriyar Hobahiya, Hakkoz da Barzillai (wanda ya auri diyar Barzillai mutumin Gileyad da ake kuma kira da wannan suna).Waɗannan sun nemi sunayen iyalansu a cikin littafin da ake rubuta sunayen amma ba su ga sunayensu ba, saboda haka sai aka hana su zama firistoci domin an ɗauka su marasa tsabta ne.Gwamna ya umarce su cewa kada su ci wani abinci mai tsarki sai firist ya yi shawara ta wurin Urim da Tummim tukuna.Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360,ban da bayinsu maza da mata 7,337; suna kuma da mawaƙa maza da mata 200.Suna da dawakai guda 736, alfadarai 245,raƙuma 435, da jakuna 6,720.Sa’ad da suka isa haikalin Ubangiji a Urushalima, sai waɗansu shugabannin iyalai suka yi bayarwar yardar rai ta gudummawarsu domin sāke gina gidan Allah a wurin da yake.Bisa ga ƙarfinsu suka bayar da darik 61,000 na zinariya, da maina 5,000 na azurfa, da rigunan firistoci guda 100.Firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali, tare da waɗansu mutane, da dukan sauran Isra’ilawa suka zauna a garuruwansu.